Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta Samu Sabon PM

Dubban Mutane ne suka ci gaba da zanga zanga a Dandalin Tahrir, dake Alkahira babban birnin kasar Masar, inda suke bukatan Gwamnatin sojin kasar ta mika mulki nan take, kamar yadda limamin da ya yi hudubar Jumma’a a Dandalin, Sheikh Mazhar Shahin ya bayyana.

Reuters
Talla

Shima limamin Masallacin Jami’ar Al Azhar, ya yi Allah wadai da nadin Kamal al-Ganzuri, mai shekaru 79 a matsayin sabon Prime Minista.

Sojojin da suka karbi iko bayan faduwar gwamnati Hosni Mubarak ranar 11 ga watan Febrairu suna karkashin matsin lamba na su mika mulki wa farar hula nan take. Majalisar soja mai mulkin kasar ta amince da nadin Kamal Ganzouri a matsayin PM, kuma ya rike wannan mukami daga shekarar 1996-1999 karkashin mulkin Mubarak. Cikin wannan makon gwamnatin PM Essam Sharaf ta yi murabus.

Gwamnatin mulkin sojan kasar ta Masar ta ce tana shirin mika mulki wa farar hula, abun da zai faro daga zaben 'yan majalisu da aka shirya gudanarwa ranar Litinin mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.