Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar zata nemi sasantawa da kamfanin hako Mai na China

Hukumomin kasar Nijar sun sha alwashin yin bincike, don gane hakikanin gaskiyar kudaden da aka kashe wajen gina matatar man Fetir, karkashin shirin hadin gwiwa da wani kamfanin kasar China na CNCP.

Tutat kasar Jamuhuriyyar Nijar
Tutat kasar Jamuhuriyyar Nijar RFI
Talla

Wannan na zuwa kafin kaddamar da sabuwar matatar Mai a birnin Zindar a ranar litinin.

A cewar Lawan Gaya, Kakakin ma’aikatar ma’adinai, zasu diba yarjejeniyar ne da Kamfanin na China idan suka samu sabani kan kudin yarjejeniyar zasu yi kokarin komawa a Teburin sasantawa da kamfanin.

Da farko Gwamnatin Nijar ta shirya ne da kamfanin akan kudi dala miliyan 600 wajen gina matatar, amma kuma daga baya Farashin ya haura zuwa dala Miliyan 980.

A shekarar 2008 ne kamfanin kasar na China ya amince da yarjejeniyar da kasar Jamhuriyyar Nijar domin gina Matatar Mai tare da hako danyen mai a yankin Agadem domin fara shiga kasuwar mai nan bada jimawa ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.