Magoya bayan Tsohon Shugaban Cote d'Ivoire Gbagbo sun ji dadin rashin fitowar masu zabe
An smau karancin fitowar masu zabe, yayin zaben ‘yan majalisun kasar Cote d’Ivoire da aka gudanar ranar Lahadi da ta gabata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mai magana da yawun jam’iyyar tsohon Shugaban kasar Laurent Gbagbo, mai suna Justin Kone Katinan ya ce wannan zai tabbatar da rashin ingancin gwamnatin Shugaba Alassane Ouattara.
Hukumar zaben kasar ta Cote d’Ivoire ta bayyana cewa an samu fitowar masu zabe na kusan kashi 35 cikin 100.
Jam’iyyar tsohon Shugaba Gbagbo tana kauracewa zaben domin nuna rashin jin dadin yadda aka mika Gbagbo wa kotun duniya dake hukunta masu laifukan yaki dake birnin Hague.
Cikin tsakiyar wannan makon ake saran samun cikekken sakamakon zaben. Dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen duniya suna gudanar da sintiri domin tabbatar da zaman lafiya tare da 'yan sandan kasar. Kuma babu wani rohoto na tashin hankali kawo yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu