Isa ga babban shafi
SUDAN

Rikici ya barke a Kordofan kudancin Sudan, Mutane 19 sun mutu

An yi wata arangama tsakanin dakarun kudancin Sudan da ‘Yantawaye a yankin Kordofon, inda dakarun Gwamnati 19 suka mutu. Kakakin ‘Yantawaye Arnu Ngutulu ya shaidaya Kamfanin Dillacin labaran Faransa AFP cewa rikicin ya barke ne a Warni kauyen Talodi da ke kudanci, kuma mutane 19 suka mutu sanadiyar barin wuta tsakanin ‘Yantawayen da dakarun gwamnati. 

Dakarun kudancin Sudan
Dakarun kudancin Sudan Reuters
Talla

Sai dai har yanzu Gwamnatin kasar Sudan ba tace komi ba akan lamarin.

A cewar Mista Lodi har yanzu ana ci gaba da barin wuta a yankin Taruje kusa da kan iyakar Kudancin Sudan, yankin da ‘Yantawayen suka mamaye tare da korar dakarun gwamnati a yankin Abu al Hassan.

Hukumar ‘Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace adadin ‘Yan gudun Hijira daga Sudan zai haura 100,000 kafin karshen Shekarar nan inda yanzu mutane 80,000 suka kauracewa yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.