Isa ga babban shafi
Janhuriyar Demokaradiyar Congo

Shugaban Congo Kinshasa Joseph Kabila ya amince da kurakurai yayin zabe

Shugaban kasar Janhuriyar Democradiya ta Congo Joseph Kabila yau Litinin ya amince da cewa akwai kurakurai a zaben kasar da ya gabata, inda ya sami zarcewa da mulkin kasar na wa'adin wasu shekaru biyar.

Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo
Joseph Kabila shugaban kasar Janhuriyar Demokaradiyar Congo AFP/Gwenn Duborthomieu
Talla

Shugaban na fadi haka ne a tattaunawa da manema labarai a Kinshasa fadar gwamnatin kasar.

Shugaban na maida martani ne game da kushe zaben da ake tayi ciki har dasu kasar Faransa da wata kungiya da tsohon Shugaban kasar Amirka Jimmy Carter ke shugabanta. Kuma ya ce zaben yafi na shekara ta 2006 inganci, duk da ya ke ba za ace an samu nasara kashi 100 ba.

Shugaba Kabila wanda ya ke kan madafun iko tun shekara ta 2001, bayan mutuwar mahaifinsa Laurent Kabila, yayin zaben da ya gabata, hukumar zabe ta aiyana shi a matsyain wanda ya lashe zabe, yayin da dadadden madugun 'yan Etienne Tshisekedi ya zo na biyu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.