Isa ga babban shafi
2011

Shekarar 2011 ta bar baya da kura

Shekarar 2011 ta bar baya da kura musamman zangar zangar kasashen larabawa da matsalarar tattalin arziki a kasashen Turai da bala’in tsunami da ambaliyar ruwa da kuma mutuwar shugaban Al Qaeda Osama bin Laden wanda dakarun Amurka suka kashe. A Najeriya kuma Gwamnatin kasar ta kasa shawo kan Matsalar Boko Haram.

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad sun yi da'ira a kasar Syria
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad sun yi da'ira a kasar Syria REUTERS/Handout
Talla

Ga muhimman abubuwan da suka faru tun farko shekerar 2011 har zuwa karshenta.

Da farko a ranar 14 ga watan Janairu ne zanga-zangar adawa da gwamnati ta barke a kasar Tunisia inda ta yi sanadiyar kifar da gwamnatin Zainul Abidina Ben Ali wanda ya kwashe tsawon shekaru 23 yana shugabancin kasar. A kasar Tunisia Majalisar Dinkin Duniya tace mutane kimanin 300 ne aka kashe a lokacin gudanar da zanga-zangar tabbatar da Demokradiyya a cikin kasar. Kuma yanzu haka jam’iyyar Musulunci ce ta Ennahda ta samu rinjayen kujeru a majalisar kasar bayan gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Octoba.

A ranar 11 ga watan Fabrairu ne irin wannan zanga zangar ta barke a kasar Masar a dandalin Tahrir a birnin alkahira, zangar da kuma ake ci gaba da yi yanzu haka bayan kifar da gwamnatin Hosni Mubarak inda ya mika mulki ga sojin kasar.

An bayyana cewa mutane 850 ne aka kashe sanadiyar zanga zangar. Yanzu haka dai tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak yana fuskantar shari’a a kasar, inda kuma al’ummar kasar ke ci gaba da nuna adawa da gwamnatin soji bayan gudanar da zaben ‘Yan Majalisu,

Bayan kasar Masar wannan zangar zangar ta adawa da gwamnatoci a kasashen larabawa ta bazu zuwa kasashen Bahrain da Syria da Yemen, amma a ranar 15 ga watan Fabrairu ne zanga-zangar ta barke a birnin Benghazi na kasar Libya inda ta yi sanadiyar kawo karshen mulkin shekaru 42 na kanal Kaddafi.

Tutar Kasar Libya
Tutar Kasar Libya

A ranar 19 ga watan Mayu ne manyan kasashen Turai wato Faransa da Birtaniya hadi da Amurka suka kaddamar da hare hare ta sama domin taimakawa ‘Yan tawaye kafin hannunta yakin ga kungiyar NATO. An kwashe tsawon watanni 9 ana gudanar da zanga a kasar Libya kafin ranar 20 ga watan Octoba inda ‘Yan tawayen kasar suka kashe Kanal Ghaddafi tare dansa Mutassim da nuna gawarsa a bainar Jama’a.

To bayan kwashe watanni guguwar neman sauyi na kadawa a kasar Yemen, sai a ranar 23 ga watan Nuwamba ne Shugaba Ali Abdallah Saleh ya amince ya mika mulki ga mataimakinsa bayan kwashe tsawon shekaru 33 yana shugabancin kasar. Yanzu haka kuma a ranar 10 ga watan Disemba ne aka rantsar da Gwamnatin hadin kai a kasar. Daruruwan mutane ne suka mutu, shi kansa shugaban kasar Abdalla Saleh bai tsaira ba domin har yanzu yana jinya bayan dala masa bom a fadarsa.

Irin wannan zangar zangar ce dai ake ci gaba da gudanarwa kasar Syria ta adawa da gwamnatin shugaba Bashar Al Assad. Kuma a watan Nuwamba ne kungiyar kasashen Larabawa ta dakatar da Syria daga kungiyar amma a ranar 19 ga watan Disemba ne Syria ta amince da wakilan kasashen larabawa cikin kasar domin diba halin da ake ciki tare da nemo hanyoyin da za’a yi sulhu.

20:05

2011: Muhimman Abubuwan da suka Faru

A shekara ta 2011 kasashen Turai sun yi fama da matsalar tattalin arziki, kuma kasar Ireland ce matsalar ta fara shafa kafin matsalar ta shafi kasar Girka da kasar Italiya. Kuma wannan matsalar ce ta yi awon gaba da Fira ministan kasar Girka George Papandreou wanda ya fusknaci matsin lamba daga sauran kasashen Turai masu amfani da kudin Euro. akan haka ne kuma mataimakin bankin Turai Lucas papademos ya karbe mukaminsa a ranar 9 ga watan Nuwamba.

A kasar Italiya ma wannan matsalar ce ta shafi Silvio Berlusconi bisa dimbim bashin da ake bin kasar. Mario Monti ne ya karbe mukaminsa a ranar 12 ga watan Nuwamba.
A cikin wannan matsalar ne kasashen Turai suka nemi taimakon kasar China domin tallafa masu fita daga cikin wannan kanki.

A ranar 9 ga watan Disemba ne kasashen Turai suka amince da wata sabuwar yarjejeiya domin ceto darajar kudin Euro matakin da ya sabawa kasar Birtaniya inda ta yi barazanar ficewa daga kungiyar kasashen.

bayan rikicin tattalin arziki tsakanin kasashen Turai, a ranar 11 ga watan Mayu akwai bala’in tsunami da girgizan kasa da aka samu a yankin arewacin Japan a cibiyar samar da makamashi nukiliya ta Fukushima al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane tare da salwantarsu kusan su 20,000.

A ranar 2 ga watan Mayu ne kuma dakarun Amurka suka cim ma burinsu na kisan Shugaban Al Qaeda Osama Bin laden a wani gidansa da yake buya a kasar Pakistan. Sai dai a lokacin Amurka ta fuskanci suka game da rashin nuna hutunan gawar shugaban domin tabbatar wa duniya sun kashe shi. Kodayake daga bisani kungiyar Al kaida ta tabbatar da mutuwar shugabansu.

Bayan mutuwar Osama, a ranar 14 ga watan Mayu akwai Maganar zargin Dominique Strauss-Kahn tsohon shugaban hukumar bada lamuni ta duniya wanda aka zarga da yiwa wata mata Nafisatu Diallo fyde ma’aikaciyar Otel a birnin New York. An dade ana sha’ria kafin watsi da zargin da ake masa.

Zargin Dominique Strauss-Kahn na zuwa ne bayan bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar Faransa domin kalubalantar shugaba Sarkozy.

Bayan nan kuma a ranar 26 ga watan Mayu ne aka cafke Ratko Mladic, mutumin da ake neman ruwa a jallo a Nahiyar Turai.

A ranar 9 ga watan Yuli ne kudancin Sudan ta balle daga Arewacin Sudan bayan gudanar da zaben raba gardama a watan Janairu inda kashi 99 na ‘yan kasar suka kada kuri’ar amincewa da samun ‘yancin yankin na kudanci.

A ranar 22 ga watan Juni ne shugaban Amurka Barack Obama ya yanke hukuncin janye dakarun kasar kimanin 33,000 daga Afganistan kafin tsakaniyar shekarar 2012. Inda a ranar 17 ga watan Juli Afghanistan ta fara daukar alhakin tafiyar da sha’anin tsaro a cikin kasar kafin ranar 20 ga watan Satumba inda aka kashe tsohon shugaban kasa Barhadudin Rabbani wanda shugaba Hamid karzai ya durawa alhakin jagorantar sasantawa da kungiyar Taliban.

A ranar 4 ga watan Ogusta ne kuma ‘Yan sandan Birtaniya suka bindige wani yaro dan shekaru 29 na haihuwa a Tottenham, al’amarin da ya haifar da tanzoma a sassan yankunan London. Mutane biyar ne dai suka mutu sanadiyar tanzomar amma daruruwan shaguna ne aka wawashe tare da kwasar ganima.

A ranar 23 ga watan Octoba sama da mutane 600 suka mutu sanadiyar wata girgizan kasa mai karfin maki 7 a gabacin Turkiya.

A ranar 31 ga watan Octoba ne Falesdinawa suka samu wakilci a hukumar al’adu da ilimi ta UNESCO a majalisar Dinkin Duniya duk da tankiyar Amurka da kasar Isra’ila.

A ranar 31 ga watan Octoba ne kuma aka bayyana cewa yawan al’ummar duniya sun kai yawan mutane Biliyan 7.

A ranar 7 ga watan Nuwamba ne wata Kotun Amurka ta yanke hukuncin daurin shekaru 4 ga likitan Micheal Jackson bayan kama shi da laifin sakaci da lafiyar mawakin kafin ya mutu.

A ranar 8 ga watan Nuwamba ne kuma hukumar makashi ta Majalisar Dunkin Duniya ta bayyana damuwa game da shirin makamashin Nukiliyar kasar Iran al’maarin da ya kai kasashen yammaci suka karfafa takunkumi ga gwamnatin kasar.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne matasa suka kai hari a ofishin jekadancin kasar Birtaniya a Tehran domin fusata ga takunkumin da aka kaubawa Iran. Daga bisani ne kuma Birtaniya ta kori jekadan Iran tare da rufe ofisin jekadancinta don mayar da martani.

A ranar 16 ga watan disemba an samu wata ambaliyar ruwa a kasar Philippines da ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000

A ranar 17 ga watan Disemba ne kuma Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Il ya mutu yana da shekaru 69 na haihuwa sanadiyar ciwon zuciya, bayan mutuwarsa kuma aka nada dansa Kim Jong-Un matsayin sabon shugaban kasa.

A ranar 18 ga watan Disemba ne kuma dakarun Amurka suka fice daga kasar Iraqi bayan kadddamar da yaki shekaru 9 da har ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin Saddam Hussian.

Ba mu san abinda zai faru ba a shekara ta 2012, ko Bashar Assad zai bada kai a Syria? yaya kuma zata kaya a zaben kasar Faransa da Amurka? Ko Sarkozy da Obama zasu kai labari?

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.