Isa ga babban shafi
Rwanda-Congo

‘Yantawayen Hutun Rwanda sun kashe mutane 26 a Congo

Jami’an tsaro a kasar Jamhuriyar Congo sun ce akalla mutane 26 ‘Yan Tawayen Hutun kasar Rwanda suka kashe, a hare haren da suke kai wa dakarun kasar tun farkon shiga sabuwar shekara.Mai Magana da yawun sojin kasar, Col Sylvain Ekenge, yace yawancin hare haren da ‘Yan Tawayen suka  kai an kai su ne da dare. 

'Yan tawayen Hutu a kasar Rwanda looacin da suke neman mafaka bayan wani samame da dakarun Rwanda da Congo suka kai masu
'Yan tawayen Hutu a kasar Rwanda looacin da suke neman mafaka bayan wani samame da dakarun Rwanda da Congo suka kai masu REUTERS/Finbarr O"Reilly
Talla

A cewarsa an kai hare haren ne a kauyen Shabunda kudancin Kivu yankin da ya yi fama da rikici bayan kawo karshen yakin basasa shekaru takwas da suka gabata inda mutane sama da Miliyan 5 suka mutu.

‘Yan tawayen wadanda suka yi ikirarin kaddamar da yaki domin kifar da gwamnatin kasar Rwanda, sun ne ‘Yan tawayen da suka rage a gabacin Congo kuma ana zarginsu da aikata miyagun laifuka da suka shafi kisa da fyade.

Ko a watan Oktoban bara an samu mutuwar mutane 10 a yankin Kivu, kuma mata sama da 170 ne aka yi wa fyade a watan Yuni.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.