Isa ga babban shafi
Najeriya

A Nigeriya sabbin hare hare a jihar Gombe

A Nigeria, wasu ‘yan bindiga da aba san ko waye ba sun kai hari a jiya da dare a wata mashaya da ke cike da mutane, a unguwar BCJ cikin garin Gombe da ke yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka kashe mutane 2, tare da raunata wasu da dama. A jihar Adamawa da ke makwbata da Gomben, an kafa dokar hana yawo a wasu kananan hukumomi, sakamakon tashe tashen hankulan da aka samu. Kananan hukumomin da lamarin shafa sun hada da Numan, Girei, Guyuk da Lamurde.Tashe tashen hankulan na jihar Adamawa sun yi sanadiyyar kone konen gidaje a garin Gbalam da ke karamar hukumar Numan. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.