Isa ga babban shafi
Najeriya

An dakatar da kwamishinan ‘Yan sanda bayan sulalewar dan Boko Haram

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Hafiz Ringim ya dakatar da kwamishinan Yan Sanda Zakari Biu, bayan tserewar wani da ake zargi da hannu wajen kai harin Bom na Madalla, wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama.

Babban sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Hafiz Ringim
Babban sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Hafiz Ringim National Daily
Talla

Kakakin rundan ‘Yan Sandan, Olusola Amore, ya ce umurnin dakatarwar ya biyo bayan zargin sakaci da ake wa ‘Yan Sandan a karkashin Zakari Biu, abinda ya sa wanda ake zargin Kabiru Sokoto sulalewa.

Bayan cafke Kabiru Sokoto da ake zargi da kitsa harin Madalla, aka mika shi hannun ‘Yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike.

Kabiru Sokoto ya sulale ne bayan da wasu da ake zargin ‘yayan kungiyar Boko Haram ne suka kai farmaki ga tawagar ‘yan sandan da ke dauke da Malam Kabiru.

Rundunanr ‘Yan sanda kasar tace wannan sakaci ne na kwamishinan ‘Yan sandan kafin daukar matakin dakatar da shi daga aikin shi.

Akalla mutane 44 ne suka mutu a harin bom da aka kai a ranar kirsimeti dai dai da wani wurin ibadar Kiristoci a Madalla kusa da Abuja.

01:12

Shaidun gani da Ido a Damaturu

Bayan kai Harin ne Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin kai shi.

An dade dai ana zargin kungiyar Boko Haram da kai hare hare a Najeriya, amma yanzu haka shugaban kasar Goodluck Jonathan ya bukaci taimakon kasashen duniya wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Sai dai wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘Yan bindiga a Maiduguri suka harbe mutane hudu har lahira, cikinsu har da sojojin dake aikin samar da tsaro a jahar.

00:32

Jekadan Nijar a Tarayyar Najeriya

Kasashen da ke makwabtaka da Najeriya yanzu haka rikicin Boko Haram ya shafe su musamman kasashen Kamaru da Nijar da ke makwabtaka da kasar a yankin Arewaci.

Jekadan Jamhuriyar Nijar a Najeriya, Mansur Mamman Haji Dodo yace gwamnatin Nijar zata karfafa matakan tsaro saboda zargin shiga da makamai daga Najeriya, da matsalar Boko Haram.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.