Chadi
Shugaban Chadi ya sallami Ministoci biyu
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya fatattaki manyan ministoci biyu daga gwamnati, sakamakon takaddama kan yarjejeniyar gina matatan man fetur da kasar China.
Wallafawa ranar:
Talla
An maye gurbin Mahamat Ali Hassa Ministan Tsare Tsare da Bedouma Karje Mataimakin Shugaban Bankin Raya kasashen Afrika, yayin da Ministan Albarkatun man fetur Tabe Eugene aka maye gurbinsa da Brahim Al Khallil wanda kafin nasa shi mukamun ke zama daraktan kula da makarantu.
Gwamnatin kasar ta Chad ta dauki matakin kan yadda takaddamar ke shafan dankatakarta da kasar China.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu