Isa ga babban shafi
Senegal

Shugaba Wade na Senegal ya fara yakin neman zabe cikin rudani

An kaddamar da yakin neman zaben Shugaban kasar Senegal da za a gudanar ranar 26 ga wannan wata na Febrairu.Cikin makonnin da suka gabata an samu zanga zanga domin nuna adawa da shirin Shugaba Abdoulaye Wade dake neman wa’ani na uku na wasu shekaru biyar. 

Reuters/Gabriela Barnuaevo
Talla

Tuni Shugaba Wade dan shekaru 85, ya yi watsi da matsin lambar kasashen duniya, inda ya ce 'yan Senegal ke da tacewa kuma su ake mulki. Amma matakin na Wade na sake takara a karo na uku, ya janyo suka da fusata daga kungiyoyin kare demokaradiya dana fararen hula.

Tuni ‘yan adawan kasar ta Senegal suka amince da shirin fahimtar juna domin kawar da Wade daga madafun iko, yayin da yake ci gaba da neman makalewa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.