Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na hasarar gangar mai 150,000 a rana, inji Shell

Katafaren Kamfanin hakar man Shell, ya ce Najeriya na hasarar ganga 150,000 na man kasar da ake hakowa kowacce rana, saboda yadda barayi ke sace man. Mataimakin shugaban kamfanin Shell mai kula da Nahiyar Afrika, Ian Craig, yace an samu raguwar masu fasa bututun mai, amma satar man na ci gaba da karuwa

Mataimakin shugaban kamfanin Shell mai kula da Nahiyar Afrika, Ian Craig,
Mataimakin shugaban kamfanin Shell mai kula da Nahiyar Afrika, Ian Craig, REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A cewar Mista Craig Najeriya na hasarar kashi bakwai cikin dari a rana.

Najeriya ta dade tana fama da ‘Yan fashin bututun mai a yankin Niger Delta wanda ke haifar da hasarar miliyoyin gangar mai a rana

Amma Mista Craig Yace, bayan an yi nasarar shawo kan fasa bututun mai, yanzu wannan matsalar ce ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

Mataimakin shugaban yace, bayan goyan bayan da barayin man ke samu a gida, suna kuma da masu taimaka musu daga kasashen waje, ta hanyar sayen man.

Kafin mutuwarsa, Tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’adua ya yi zargin manyan kasashen duniya da tallafawa barayin, wajen sayen abinda ya kira man da aka gurbata shi da jini.

Hukumar kula da makamashi a Najeriya, tace a halin yanzu kasar na hako gangar mai Miliyan biyu da dubu dari da tamanin kowacce rana, yayin da cin hanci da almundahana da rashin gaskiya ya dabaibaye aikin samar da man.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.