Libya
Shugabannin Kabilun Libya na Tattauna hanyar magance rikice rikice
Shugabannin Kabilun dake Libya, na tattaunawa dan kawo karshen tashin hankalin da ake samu a Kudu maso Gabashin kasar, wanda ya haifar da mutuwar mutane da dama.
Wallafawa ranar:
Talla
Abubakar Sadep, daga kabilar Tibu, ya ce yanzu haka shugabanin na garin Kufra, inda suke tattaunawa da bangarorin kabilun kasar.
Rikice rikice sun zama ruwan dare cikin kasar ta Libya inda kungiyoyi masu dauke da makamai ke cin karensu babu babbaka, tun bayan yakin basasan shekarar data gabata, wanda ya yi saniyar kawar da gwamnati Marigayi Muammar Gaddafi ta shekaru 42 daga madafun iko.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu