Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan sandan Najeriya sun ce Abu Muhammad ya mutu

‘Yan Sanda a Najeriya sun sanar da mutuwar Abu Muhammad bayan fama da raunin harsashen Bindiga wanda ake zargin jagoran yin garkuwa da Turawan Birtaniya da Italiya wadanda suka mutu a Najeriya.

Wasu da ba'a tantance ko 'yan kungiyar Boko Haram ne wadanda ake zargin sun yi garkuwa da Turanwan Birtaniya da Italia Chris McManus da  Franco Lamolinara
Wasu da ba'a tantance ko 'yan kungiyar Boko Haram ne wadanda ake zargin sun yi garkuwa da Turanwan Birtaniya da Italia Chris McManus da Franco Lamolinara REUTERS/Stringe
Talla

‘Yan sandan sun ce Abu Muhammad ya mutu ne a ranar 9 ga watan Maris sanadiyar harsashen bindigar da aka harbe shi a lokacin da ‘Yan sanda suka kai samame a Zaria a ranar 7 ga watan Maris.

‘Yan sandan sun ce Turawan sun mutu ne a garin Sakkwato Arewa maso yammacin Najeriya a ranar 8 ga watan Mayun bara.

A cewar ‘Yan sandan Najeriya, sun kai samamen ne a garin Zaria a ranar Laraba 7 ga watan Maris kwana daya kafin a cafke Abu Muhammad da wasu mutane guda biyar.

A ranar Laraba ne aka gabatar da Abu Muhammad ga ‘Yan Jarida inda aka nuna su cikin rauni.

Samamen da Fira ministan Birtaniya David Cameron ya bayar da umurni ya nemi saba dangantar Diflomasiya tsakanin Ingila da Italiya, inda Italiya tace ba ‘a sanar da ita ba kafin kaddamar da kai harin.

Gwamnatin Najeriya dai ta fuskanci matsin lamba da kalubale game da lamarin, kuma masana da dama sun bayyana shakkunsu da damuwa akan alakanta garkuwa da Turawan ga Kungiyar Boko Haram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.