Isa ga babban shafi
ECOWAS-Mali

Ouattara zai jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Mali

A yau Alhamis ne Shugabannin kasashen Afrika guda shida na kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin Alassane Ouattara shugaban kasar Cote d’Ivoire zasu kai ziyara kasar Mali domin tattauna yadda za’a dawo da mulkin kasar karkashin kundin tsarin mulki bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Farar Hula ta Amadou Toumani Toure.

Taron kasashen ECOWAS game da hambarar da shugaban Mali Amadou Toumani Touré, wanda aka gudanar a birnin  Abidjan.
Taron kasashen ECOWAS game da hambarar da shugaban Mali Amadou Toumani Touré, wanda aka gudanar a birnin Abidjan. REUTERS/Thierry Gouegnon
Talla

Hambararren shugaban kasar Amadou Toure wanda har yanzu ba a san mabuyarsa bat un bayan kifar da gwamnatinsa a ranar 22 ga watan Mayu, a jiya Laraba ya shaidawa Rediyo Faransa cewa yana cikin birnin Bamako kuma cikin koshin Lafiya amma ba hannun Soji ba.

Ziyarar shugabannin ECOWAS na zuwa ne bayan dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan gwamnatin Sojin Mali.

Tuni dai Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ta dakatar da wakilcin kasar Mali a kungiyar saboda juyin mulkin da Sojoji suka yi na hambarar da gwamnatin Farar hula ta Amadou Toumani Toure.

Kungiyar ta cim ma matakin tura wasu Wakilanta Zuwa Mali domin tattauna yadda za’a dawo da kasar tafarkin demokradiyya.

Sai dai kuma a kafar Telebijin, gwamnatin Sojin Mali ta bayyana sabon Kundin tsarin mulkin kasar wanda ya kunshi ‘Yancin Fadin albarkacin baki da zirga-zirga.
Kuma bubu wani tabbaci da Gwamnatin Soji ta bayar game da mayar da gwamnatin da aka hamabarar ta Farar hula, kamar yadda masu makwabtaka da kasar suka bukata.

Sojojin kasar sun hambarar da gwamnatin Amadou Toumani Toure ne saboda rashin gamsuwa da tsarin shi na magance rikicin ‘Yan tawayen Azbinawa a Arewacin Mali.

Matakin dakatar da Mali daga ECOWAS ya biyo bayan wani taron gaggauwa ne da shugabannin kungiyar suka gudanar a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire.

Ana sa ran tawagar ECOWAS zata kunshi shugabannin kasashen Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara da shugaban kasar Benin da Burkina Faso da Nijar da Liberia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.