Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan ta kaddamar da hare hare a Yankunan Kudancin Sudan

Sudan ta kaddamar da wasu jerin hare hare guda biyar a kauyen Bentiu da wasu yankunan kudancin Sudan. Tuni Gwamnatin Sudan tace zata shirya dakarunta domin yaki da Sudan ta kudu tare da katse duk wata tattaunawa game da mallakar arzikin man Fetur bayan Sudan ta kudu ta mamaye yankunan da ke da arzikin mai domin durkushe tattalin arzikin Arewacin Sudan.

Shugaban kasar Sudann Omar Bashir da Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir lokacin a birnin Khartoum
Shugaban kasar Sudann Omar Bashir da Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir lokacin a birnin Khartoum
Talla

Tuni Sudan ta kudu ta zargi Sudan wajen kai hare hare a kauyukan da ke akan iyaka da kasashen biyu.

Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun yi kiran kawo karshen rikicin kasashen biyu.

An kwashe lokaci mai tsawo bangarorin biyu suna rikici game da mallakar yankunan da ke da arzikin man Fetir, bayan samun ‘yancin Yankin kudanci daga Sudan.

A ranar Talata Sudan ta kudu ta kaddamar da hare hare a yankin Heglig, yankin da ke samar da gangan mai 115,000 a rana. Kuma yanzu dakarun SPLA sun yi ikirarin karbe ikon yankin.

Gwamnatin Amurka ta aiko da sakon yin Allah waddai da harin Kudancin Sudan.

Jekadan Sudan a Majalisar Dinkin Duniya Daffa-Alla Elhag Ali Osman yace idan Majalisar Dinkin Duniya ba ta la’anci harin Sudan ba tare da kiran gaggauta ficewa da dakarunta, to dole Sudan ta mayar da martani.

A bara ne yankin kudanci ya balle daga Sudan amma har yanzu babu wata sasantawa da bangarorin biyu suka cim ma game da raba arzikin kasar.

Yanzu haka kuma Sudan tace zata yi watsi da duk wani yunkurin tattaunawa a teburin sasantawa da Kudancin Sudan karkashin jagorancin kungiyar Tarayyar Afrika.

Rehotanni daga zauren Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa, Ban Ki-moon ya zanta da Shugaban Kudancin Sudan Salva Kiir inda ya nemi tsagaita wuta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.