Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan zata kori ‘Yan kudancin Sudan 12,000

Gwamnatin Sudan ta bada wa’adin mako daya ga ‘Yan kudancin Sudan 12,000 domin  ficewa daga kasar Tare da kafa dokar hana fita akan iyakokin kasashen Biyu. A yau Litinin ne Majalisar Sudan zata yi muhawara akan kudirin dokar katse hulda da Sudan ta Kudu.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir Reuters
Talla

Gwamnan Jahar White Nile Yusuf Al-Shambali, yace an shata ranar Biyar ga watan Mayu ga kabilun Kudancin Sudan domin su fice.

Gwamnan yace ya zamo wajibi ga kabilun da ke ci gaba da samun matsugunni a Kosti su fice a yankin ko gwamnatin Jahar ta san yadda zata yi dasu.

A cewar mista Shambali, ci gaba da zamansu a wannan tsibiri, babbar barazana ce ga tsaron kasar Sudan da al’ummar Kosti.

Mutanen suna daga cikin ragowar mutune 350,000 da Ofishin jekadanci kasar Sudan ta kudu ya kiyasta suka rage a yankin Arewaci, bayan wa’adin ranar 8 ga watan Afrilu da aka shata masu game da matsayin dawo wa gida ko ci gaba da zama a Sudan.

Babbar Jami’ar hukumar kula da ‘yan gudun Hijira Jill Helke, tace wannan ne karon farko da Gwamnan Jahar ya bayar da wannan umurni a kokarin da ake na kwashe mutanen.

Tace hukumar ta samar da kudaden safarar mutane 7000 zuwa Sudan ta Kudu, amma tace hukumar tana neman wasu kudaden don kwashe wasu mutane 5000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.