Isa ga babban shafi
Senegal

An buda bikin nuna al'adun sana'oin hannu na Afrika a kasar Senegal (Dak’Art)

A yau juma’a shugaban kasar Senegal Macky Sally a buda soma wani gawurtacen bikin al’adu na kirkire kirkiren ayukan hanu na nahiyar Afrika a birnin Dakar babban birnin kasar ta Senegal (Dak’Art).Bikin da za a share tsawon wata guda ana yi, ya samu halartar masu raya al’adun ta fannin kere keren hannu su 42 da suka fito daga kasashe 21 na nahiyar Afrika, da kuma na tsibirin Renion, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Fransa ya sanar.A lokacin da yake jawabin buda taron, shugaba Macky Sall ya bayyana cewa, shagulgulan al’adun na (Dak’Art) shagulgula ne, masu matukar muhimmanci, inda kowa zai nuna kwarewarsa ta hanyar kere-kiren hannu, da kuma nuna basira wajen ciyar da al’adun nahiyar Afrika gaba 

REUTERS/Joe Penney
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.