Isa ga babban shafi
Algeria-France

kasar Algeria ta fara lalata nakiyoyin da Fransa ta bibbine mata a lokacin yakin kasar na 1954 zuwa 1962

Kamfanin dillancin labaran kasar Aljeria ASP ya bayyana cewa a cikin watan Avrilun da ya gabata dakarun Sojan kasar sun lalata kimanin nakiyoyi dubu 4.295 a kan iyakokin dake yankin yammacin kasar, a karkashin wani katafaren aiki da suke yi na tsabtace yankin, da dakarun kasar Fransa suka bibbine nakiyoyi a lokacin yakin neman yancin kan kasar ta Aljeria na 1954-1962.

sojojin Fransa sun kai wani gagarumin hari  a ranar 1 ga watan november  na 1954 kasar  Algérie,
sojojin Fransa sun kai wani gagarumin hari a ranar 1 ga watan november na 1954 kasar Algérie, AFP
Talla

Wannan sabon aiki na lalata nakiyoyin ya sa jimalar nakiyoyin da aka lalata suka kai guda dubu 627.914 dubu 531-434 na kai hari ne a kan mutum guda a yayinda wasu dubu 92.505 na tarwatsa gungun jama’a ne, sai kuma guda dubu 3.975 da ake wargaza motoci da su.
 

Yanzu haka ana ci gaba da tonon kimanin nakiyoyi milyan uku, daga cikin miliyan 11 da Fransa ta daddasa a duk tsawon yankin kan iyakar gabashi da yammacin kasar Aljeria, kamar yadda wani jami’in sojan Algeria ya bayyana a watan janairun da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.