Isa ga babban shafi
Congo-Kinshasa

sama da mutane 100 ne aka kashe a yankin gabashin kasar jamhuriyar demokradiyar Congo

Sama da mutane 100 ne aka kashe a makon da ya gabata a yankin gabashin kasar Jamhuriyar demokradiyar Congo, a lokacin wani harin da aka dora alhakin kai shi kan kungiyoyin dakarun sa kai na mai mai da na yan tawayen kabilar Hutun kasar Ruwanda FDLR.

Au moins 200 morts en RD Congo après l'explosion d'un camion-citerne qui a mis le feu à un village du Sud-Kivu à la fontière avec le Burundi.
Au moins 200 morts en RD Congo après l'explosion d'un camion-citerne qui a mis le feu à un village du Sud-Kivu à la fontière avec le Burundi. Latifa Mouaoued/RFI
Talla

Mataimakin shugaban kungiyoyin kare hakkin dan adam a yankin arewacin Kivu na gabashin kasar Congo, ya bayyana cewa a makon da ya gabata ne, kungiyar dakarun sa kai ta mai-mai ta kai wani hari a kan yan tawayen kasar ta Runwanda FDLR wadanda su kuma suka mayar da martani ta hanyar hallaka dukkanin wani mutum da suka hadu da shi a hanya bisa zargin ya na hada kai da Mai-mai,

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, sama da mutane 100 ne aka kashe mafi yawancinsu kuma, da makaman gargajiya aka hallaka su, dangin Adda da Mashi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.