Isa ga babban shafi
Masar

Al’ummar Masar zasu kada kuri’ar zaben shugaban kasa

Al’ummar Masar zasu kada kuri’ar zaben shugaban kasa karo na farko a Tarihin siyasar kasar bayan hambarar da gwamnatin Hosni Mubarak. ‘Yan takara 12 ne ke neman kujerar shugaban kasa kuma babu wani zaben ra’ayin jama’a da ya nuna akwai wanda zai iya lashe zaben.

WAsu Al'ummar kasar Masar
WAsu Al'ummar kasar Masar REUTERS/Hani Abdulla
Talla

Sa’o’I 48 kafin yau Laraba aka haramtawa ‘Yan Siyasa yakin neman zabe.

Mutane Miliyan 50 ne dai ake sa ran zasu kada kuri’a a zaben shugaban kasa.

Duk da yake an gudanar da zaben ra’ayin Jama’a amma zaben ya nuna akwai hamayya a zaben tsakanin ‘Yan takara Hudu cikin kuma sun hada da Amr Musa da Abdel Moneim Abol Fatour da Mohammed Mursi na Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Brotherhood da kuma Ahmed Shafiq.

Da misalain karfe 8 Agogon Masar al’ummar kasar ake sa ran zasu fara kada kuri’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.