Isa ga babban shafi
Masar

Masar ta fada wani sabon rikici bayan kotu ta nemi a soke zaben ‘Yan Majalisa

Yunkurin dawo da kasar Masar karkashin mulkin Demokradiyya ya gamu da Cikas bayan da kotun koli ta nemi a soke zaben ‘Yan majalisu da aka gudanar a bara domin samun kura-kurai tare da amincewa da Ahmed shafiq a matsayin dan takarar shugaban kasa sabanin dokar da ta so hana tsohon Fira ministan kasar tsayawa takara.

Wasu Masu Zanga-zanga suna cinnawa hoton yakin neman Shafiq wuta bayan Kotun kolin kasar ta nemi soke zaben 'Yan Majalisa
Wasu Masu Zanga-zanga suna cinnawa hoton yakin neman Shafiq wuta bayan Kotun kolin kasar ta nemi soke zaben 'Yan Majalisa REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Da safiyar juma’a masu gwagwarmaya sun yi kiran wata sabuwar zanga-zanga Inda Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi tace nasarar da aka samu a zanga-zangar da ta yi sanadiyar kifar da Mubarak zata tafi a banza bayan da kotun koli ta rushe ‘Yan Majalisar.

‘Yan Siyasa dai sun ce wannan wani juyin mulki ne.

Kotun koli ta haramta dokar da ta nemi haramta Jami’an gwamnatin Mubarak tsaya takara a zabe har tsawon shekaru 10.

Karkashin dokar ne dai aka so a haramtawa Ahmed Shafiq tsayawa takara wanda shi ne Fira ministan Hosni Mubarak.

Tun kifar da gwamnatin Mubarak a watan Fabrairun bara, Sojoji suka karbi ragamar shugabancin Masar. Sai dai akwai matakai da dama da ake bi domin rushe juyin juya halin da al’ummar kasar suka shirya tun da farko.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.