Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan bai damu da ‘Yan Najeriya ba, inji ACN

Jam’iyyar adawa ta ACN a Najeriya, ta bayyana damuwa da bacin rai game da tafiyar shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zuwa wani taron kula da muhalli a kasar Brazil, a dai dai lokacin da wasu Jahohin kasar ke cin wuta. Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Majalisar wakilan kasar ta nemi bayani daga Shugaban game da halin da Najeriya ta shiga.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zatawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zatawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Sakataren Jam’iyar ACN, Sanata Lawal Shuaibu, yace akwai bacin rai domin hankalin al’ummar Najeriya a tashe ya ke amma Goodluck Jonathan ya kama hanya zuwa Brazil bayan samun tashin bama bamai a Damaturu da Kaduna.

Lawal Shu’aibu yace akwai shugabanni kasashen Duniya da Jonathan ya kamata ya yi koyi da su kamar shugaban kasar China wanda ke ziyara a yankin Latin Amurka amma ya juyo zuwa gida saboda bala’in girgizan kasa.

Mista Lawal yace Jonathan bai san makamin mulki ba, kuma shugaban ya nuna ba ya tare da al’ummar Najeriya.

A ranar Talata ne Majalisar Waikilan Najeriya karkashin Dan Majalisa Femi Gbajabiamila suka bukaci bayani daga Shugaba Jonathan akan halin matsalar tsaro da Najeriya ta shiga.

Tun a Ranar Lahadi ne Najeriya ke cin wuta bayan barkewar Rikici Addini da tashin bama bamai a Arewacin kasar wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane 95.

A ranar Lahadi wasu jerin bama bamai suka tashi a Kaduna, al’amarin da kuma ya haifar da rikicin Addini bayan tashin bamai bama-. Daga bisani kuma aka sake samun wasu jerin bama bama da harbe harben bindiga a garin Damaturu.

02:22

Rahoto daga Bauchi

Muhammad Ibrahim Bauchi

A garin Bauchi akwai labarin wani matashi da ya dala wa kansa Bom a kusa da makarantar Gwamnatin Tarayya ta Mata, kamar yadda Kwamishin ‘Yan Sandan Jahar Bauchi Mohammed Ladan ya shaidawa RFI.

A lokacin da Hon. Jerry Manwe ke bayani a zauren Majalisa, Dan Majalisar yace idan Shugaba jonathan yasa wadanda ke da hannu ga Rikicin Boko Haram ya kamata a ce an kama su.

A kan haka ne kungiyar Kiristoci ta CAN ke kalubalantar gwamnatin Tarayya game da tafiyar hawainiyar da gwamnatin ke yi wajen magance matsalar Boko Haram.

“Tun lokacin da aka fara kai hare hare, babu wani yunkuri da Gwmanatin Goodluck Ebele Jonathan ta yi domin kawo karshen zubar da jinni” inji hukumar CAN.

Babu wani lokaci da aka tsayar da Shugaba Jonathan zai gurfana gaban Majalisar Wakilai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.