Isa ga babban shafi
DRC Congo

Mummunar kwayar Cutar Ebola

Cutar Ebola na daya daga cikin munanan cututtuka da ke addabar Bil Adama wacce a yanzu haka ta ke addabar kasar Uganda.A yanzu haka babu maganinta babu kuma rigakafinta. 

Ana iya samun cutar Ebola a jikin namun daji irinsu Jemagen da ke dauke da cutar.
Ana iya samun cutar Ebola a jikin namun daji irinsu Jemagen da ke dauke da cutar. IRD/ Jean-Jacques Lemasson
Talla

Akalla mutane sama da 1,850 aka samu da kwayar cutar tun da aka gano ta shekaru 36 da su ka wuce a kasar Jamhuriyar demokradiyar Congo a lokacin ta na kasara Zaire.

Kana, 1,200 daga cikinsu sun mutu, kamar yadda wani rahoton kwamitin kiwon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

Alamun cutar sun hada da zazzabi mai zafi, ciwon jiki, kasala, amai da gudawa a wasu lokuta kuma akan samu zubar jini a wasu lokuta.

Kwararru a bangaren kiwon lafiya sun bayyana cewa, daya daga cikin hanyoyin da ake rage yaduwar cutar shine ganin cewa ta na kashe wanda ta kama nan da nan kamin ya harbi wasu.

Kamuwa da cutar da kuma lokacin da za ta mamaye jikin mutum duka akalla a kwanaki 21 na farko.

Ana kuma iya yada wannan cuta ta hanyar musayar jini, ko kuma wani nau’in ruwa na jikin wanda ya kamu da cutar.

Daya daga cikin hadarin cutar shine ko likitoci da kan gwada ko mutum na dauke da ita kan iya kamuwa a lokacin da su ke gudanar da gwajin.

An sama cutar lakabin cutar Ebola daga wani rafi da ke kasar ta Congo, ana kuma samun ta ne daga namun daji wadanda su ka kamu da cutar irinsu birrai, Jemage, da Gada ko suna mace ko a raye.

Cutar ta kashe mutane 37 a shekarar 2007 haka kuma ta kashe mutane 170 a Arewacin kasar ta Congo.

Masana da dama sun fitar da magunguna wadanda har yanzu basu yi tasiri ba.

Hanya mafi saukin kare cutar kamar yadda hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shi ne da mutum ya mutu a yi maza a binne shi ba tare da bata lokaci ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.