Isa ga babban shafi
Amruka-Afrika

Hillary Clinton ta gudanar da karin kumallon safe a gidan Nelson Mandela

Sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka uwargida Hillary Clinton ta gudanar da karin kumallon safe a yau litanin a gidan tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela, dake kauyen Qunu a kudu maso gabashin kasar, inda gwarzon yaki da wariyar launin fatar ya kaurace yana jiran ta Allah, bayan da ya share tsawon shekaru 94 ya na shakar numfashin duniya.Uwargida Clinton ta tattauna da Mr Mandela kafin cin abincin karin kumallon, a Qunu inda Mr Mandelar ya yi yaritarsa a ciki, wannan halin mutuntawa da Hillary ta nuna, zai tsaya abin tunawa ga Mandela, a daidai lokacin da koshin lafiyarsa ke dada yin rauni. 

sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Uwargida Hillary Clinton
sakatariyar harakokin wajen kasar Amruka, Uwargida Hillary Clinton
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.