Isa ga babban shafi
Najeriya

An kafa dokar hana fita a Okene ta Najeriya

Gwamnatin Jihar Kogi a Najeriya, ta kafa dokar hana fita a Yankin Okene, sakamakon kashe sojoji biyu, bayan harin da ya lakume mabiya addinin Kirista 18. Gwamnan Jihar Idris Wada, ya bukaci al’ummar Yankin taimakawa da bayanai ga shugabanni don gano masu aikata laifufukan.

Gwamnan Jahar Kogi Idiris Wada
Gwamnan Jahar Kogi Idiris Wada Nigerian eye
Talla

A ranar Litinin ne wasu ‘Yan bindiga da ba a tantance ba suka bude wuta a wata Mujami’a a Kogi inda suka bindige mutane 19 cikinsu har da Limamin mabiya addinin Kirista. A garin Okene kuma, wasu ‘Yan bindiga sun sake bindige Sojoji biyu a ranar Talata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.