Libya
Gwamnatin NTC ta mika mulki ga Majalisar Libya
Gwamnatin Rikon kwarya a kasar Libya, ta mika mulki ga zababiyar Majalisar kasar, a wani biki da aka yi a jiya Laraba, wanda ya kawo karshen juyin juya halin day a kawo karshen mulkin Kanal Gaddafi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Shugaban Majalisar Rikon kwaryar, Mustaf Abdel Jelil, yace ya mika ragamar tafiyar da kasar ga zababbiyar Majalisar da al’ummar kasar suka zaba, a karkashin jagorancin Othman Ben Sassi.
Bayan karbar rantsuwar Mulki, yanzu Majalisar kasar za ta zabi Firaminista tare da shirya zabe sannan a rushe gwamnatin NTC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu