Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Mutum 30 sun rasa rayukansu a rikicin mahaka ma’adinai a kasar Afrika ta Kudu

Akalla mutane 30 ne su ka rasa rayukansu a bayan ‘Yan sanda sun bude wuta akan wasu ‘Yan kungiyoyin mahaka ma’adinai sun kaure da fada a kasar Afrika ta kudu. Wannan arangama ba a taba ganin irinta ba tun sai a lokacin yakin wariyar launin fata da kasar ta taba fama da shi. 

'Yan sandan kasar Afrika ta Kudu a wurin da ma'aikatn hakan ma'adinai su ka yi arangama.
'Yan sandan kasar Afrika ta Kudu a wurin da ma'aikatn hakan ma'adinai su ka yi arangama. REUTERS
Talla

Ministan ‘Yan sanda kasar, Nathi Mthethwa ya bayyana hakan a gidan radiyo inda ya tabbatar da cewa mutane 30 ne su ka mutu a wajen hakan ma’adinai da ke Lonmin Marikana.

Ya kara da cewa wasu kuma da dama sun samu raunuka.

Sai dai kungiyar ma’aikatan mahakan ma’adinan ta ce mutane da su ka mutu sun kai 36.

A cewar Mthethwa, masu zanga zanga suna dauke ne da makamai da su ka hada da bindigogi suna kuma tunkararsu a lokacin da abun ya faru.

Ya kara da cewa, ba a so hakan ta faru, domin a lokuta da dama ana fada cewa wannan kasar na da dokoki wacce ta ba da dama mutane su nemi izinin yin zanga zanga ko jerin gwano a duk lokacin da su ke son yin hakan.

A cewar Mthethwa, gwamnatin kasar ba za ta yarda da gudanar da zanga zanga ba ba tare da samun izinin hukuma ba.

Tuni dai shugaban kasar, Jacob Zuma ya yanke wata tafiya da zai yi zuwa wani taro da za a gudanar a Mozambique domin ya ziyarci wurin da lamarin ya faru.

A wata takardar sanarwa da mai Magana da yawun shugaba Zuma, Mac Maharaj, ta nuna cewa, a wunin yau ne shugaban zai ziyarci wurin.

Wasu daga cikin ma’aikatan hakan ma’adinan ne su ka fara zanga zanga a ran 10 ga watan Agusta inda su ke neman a ninka musu albashinsu zuwa kashi uku, wanda hakan ya jirkic ya kuma fada tsakanin kungiyoyin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.