Habasha
A Ranar Biyu ga watan Satumba za’a binne Zenawi
Gwamnatin kasar Habasha tace a ranar Biyu ga watan Satumba za’a binne tsohon Firaministan kasar Meles Zenawi wanda ya mutu a ranar Litinin a birnin Brussels bayan kwashe lokaci yana rashin lafiya.Daruruwan Habashawa ne suka yi zaman makokin mutuwar Shugaban bayan kawo gawarsa zuwa Addis Ababa daga Brussels a ranar Talata. Yanzu haka gawarsa an ajiye ta a cikin gidansa kafin bukin binne shi.
Wallafawa ranar:
Talla
Mataimakin Firaminista Hailemariam Desalegn zai jagoranci gwamnatin rikon kwarya har 2015 bayan an gudanar da zabe. Ana sa ran rantsar da shi nan bada dadewa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu