Isa ga babban shafi
cote d'Ivoire

An cafke Akoun na hannun damar Gbagbo a Cote d’Ivoire

‘Yan Sandan kasar Cote d’Ivoire sun cafke Laurent Akoun wani babban na hannun damar tsohon shugaba Laurent Gbagbo, watanni 18 da kawo karshen rikicin siyasar kasar tsakanin shi da Alassane Ouattara.

Laurent Akoun na hannun damar Laurent Gbagbo tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire yana zantawa da manema labarai
Laurent Akoun na hannun damar Laurent Gbagbo tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire yana zantawa da manema labarai AFP/Sia Kambou
Talla

Kakakin Jam’iyyar FPI yace Akoun yana hannun ‘Yan Sanda a Abidjan. Sai dai babu wani bayani game da laifin da yasa aka cafke shi amma wata majiyar gwamnatin kasar ta ce ana zargin shi da hannu a wani harin da aka kai wa Sojan kasar.

A wannan watan akwai na hannun damar Gbagbo da dama aka Cafke.

Hukumomin kasar Ghana sun bayar da tabbacin kama Justin Kone Katinan mai Magana da yawun tsohon shugaban kasar Cote D’Ivoire Laurent Gbagbo, sai dai har yanzu ba a yanke shawarar mika shi zuwa Cote d’Ivoire.

Tun bayan da aka kifar da Gwamnatin tsohon shugaba Gbagbo, Justin Kone Katinan, wanda shi ne ministan kasafin kudi ya tsere zuwa Ghana.

Wata majiya daga gwamnatin kasar Cote D’Ivoire, karkashin Shugaba Alassane Ouattara, ta ce ana sa ran za a kai Katinan zuwa kasar, a karshen wannan makon.
Yanzu haka Gbagbo yana birnin Hague inda yake fuskantar Shari’ar zargin aikata laifukan yaki a kotun Duniya ta ICC.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.