Isa ga babban shafi
Mali

yan kasar Mali na ci gaba da yinkurin neman hanyar sasanta rikicin yankin arewacin kasar

Hadin guiwar kungiyar yan siyasar da fararen hular kasar Mali sun bayyana sakamakon haduwarsu da kungiyoyin yan tawaye da na masu kishin islama, da suka mamaye yankin arewacin kasar, dangane da fatan da kungiyar ke da shi na samun mafita rikicin ta hanyar tattaunawa.

Manzon Cedeao  Djibril Bassolé,ya sadu da  Iyad Ag Ghali, shugaban kungiyar Islama ta  Ansar Dine, a Kidal a kasar Mali.
Manzon Cedeao Djibril Bassolé,ya sadu da Iyad Ag Ghali, shugaban kungiyar Islama ta Ansar Dine, a Kidal a kasar Mali. AFP PHOTO / RPMARIC HIEN
Talla

 

manzannin hadin guiwar kungiyar hadakar yan siyasar da na fararen hular kasar ta Mali da a makon da ya gabata suka je a yankin arewacin kasar, inda suka yi nasarar ganawa da shugabanin kungiyar Ansar Dine, da na mayakan jahadi ta Mujao, tattaunawar da ta gudanar a manyan garuruwa yankin arewacin kasar ta Mali guda uku : Tombouctou, Gao da Kidal.

Wannan yinkuri na farko da yan kasar ta Mali suka yi domin samun nasarar magance matsalolinsu ta hanyar tattaunawa, ta nuna cewa, duk yadda take, ya zama wajibi a je a yankin arewacin kasar a tattauna da kungiyoyin dake dauke da makamai a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.