Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

An fara sako mahaka ma’adinan Afrika ta Kudu

Wata kotun kasar Afrika ta Kudu za ta fara sako mahaka ma’adinan kasar su 270 bayan kisan da ‘Yan sanda su ka yiwa  wasu daga cikin abokan aikinsu wanda ake zraginsu da tunzura kisan. 

Zanga- zangar da wasu 'Yan kasar Afrika ta Kudu su ka yi domin a sako, mahaka ma'adinan
Zanga- zangar da wasu 'Yan kasar Afrika ta Kudu su ka yi domin a sako, mahaka ma'adinan REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Bayan wani bore da ‘Yan kasar ta Afrika ta Kudu su ka yi ne, Shugabar shigar da kara a kasar, Nomgcobo Jiba, ta ce za ta sake duba laifukan da ake zargin mahaka ma’adinan da su.

“Laifukan kisan da ake zargin ma’aikat su 270, za a janye karar a zaman kotun da za a yi nan gaba”, inji Jiba, a hirar ta da Kamfanin Dillancin labaran AFP.

A cewar ta, a yau Litinin ne za a fara sako mahaka ma’adinan.

Ta ce tuni an riga har an tabbatar da lambobin gidan 140 daga cikin ma’aikatan inda ta kara da cewa sauran kuma nan da zuwa Alhamis duk za su tafi gida.

Ana dai tuhumar mahaka ma’adinan da laifin kisan abokanan aikinsu 34 da ‘Yan sanda su ka kashe, wanda aka daura laifin a kansu bayan zarginsu da aka yi da tunzura ‘Yan sandan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.