Isa ga babban shafi
Najeriya

Musulmin Najeriya sun gudanar da Zanga zanga saboda muzantawa Islama

Al’umar Musulmin Nigeria sun bi sahun ‘Yan uwansu a duniya wajen gudanar da zanga zanga a garin Zaria, dan nuna bacin ransu da fim din da ya ci zarafin addinin Islama. 

Tutar kasar Najeriya
Tutar kasar Najeriya www.escdijon.eu
Talla

Haka kuma zanen da aka danganta shi da Manzan Allah, wanda tsira da aminci Allah su ka tabbata a gareshi, na daya daga cikin dalilan da ya kara sa aka gudanar da Zanga zangar.

Abdurahman Suleiman Bawa na daya daga cikin wadanda suka shiga zanga zangar, ya kuma gayawa Sashin Hausa na gidan Radiyo Faransa cewa sun gudanar da Zanga zangar ne domin nuna bacin ransu ga wannan fim da kuma zane da wata mujalla ta yi a kasar Faransa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.