Isa ga babban shafi
Sudan-Sudan ta Kudu

Sudan da Sudan ta Kudu sun cim ma matakin sasanta juna

Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun kara jaddada tabbatar da dorewar zaman lafiya da kuma habaka harkokin kasuwanci a tsakaninsu a wani taro da aka gudanar a birnin Vienna, a karon farko bayan amincewa da wata yarjejeniya da kasashen biyu su ka yi a watan da ya gabata, na tabbatar da dorewar zaman lafiya a tsakaninsu.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da takwaransa  Omar al-Bashir  tare da Mbeki a tsakiya a lokacin da suka amince da wata jarjeneiya a  Addis Ababa, ranar 27 September, 2012
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da takwaransa Omar al-Bashir tare da Mbeki a tsakiya a lokacin da suka amince da wata jarjeneiya a Addis Ababa, ranar 27 September, 2012 Reuters/Tiksa Negeri
Talla

Ministocin harkokin wajen kasashen biyu, a wani taron habaka harkokin kasuwanci da aka gudanar a Vienna, sun kara jaddadawa a gaban taron cewa, za su ci gaba da aiki tare, domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

A cewar Ministan harkokin Wajen kasar Sudan, Ali Ahmed Karti, za su nemi fito da hanyoyin kauracewa barkewa rikici a tsakaninsu, tare da neman amincewa da matakin tattaunawa.
A makwanni biyu da suka shude ne, kasashen biyu suka rattaba hannayensu akan wata yarjejeniyar kawo karshen tashe tashen hankula a tsakaninsu, da kuma dawo da huldar jigilar Mai daga Sudan ta kudu inda za a bi da shi ta cikin Sudan.

Sai dai masu sa ido akan al’amuran yau da kullum na ganin akwai sauran rina a kaba, domin kasashen biyu, har yanzu ba su dauki matsaya akan yankin nan na Abyei da ake takkadma akai ba, da kuma wasu iyakokin kasashen.

Kasashen biyu dai na da tarihin yin yarjeniyoyi tsakaninsu, sai dai a wasu lokuta da dama ba kasafai su kan cika su ba.

Ko a wannan satin, sau biyu wasu masu dauke da bindiga su ka yi ikrarin kai hare hare a Jihar Kordofan da ke Sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.