Isa ga babban shafi
MDD-Mali

MDD ta amince kasashen Afrika su dauki matakin Soji a Mali

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da daftarin da zai ba kungiyar ECOWAS damar daukar matakin Soji a arewacin kasar Mali da ke karkashin ikon mayakan Ansar Dine. Kwamitin tsaron ya bukaci kasashen Afrika su gabatar masa da bayani game da kudirin na daukar matakin soji nan da kwanaki 45.

Mayakan kungiyar Ansar Dine a Arewacin Mali
Mayakan kungiyar Ansar Dine a Arewacin Mali REUTERS/Adama Diarra
Talla

A cikin bayanin Daftarin, kwamitin ya bukaci mahukuntan kasar Mali tare da shugabannin ‘Yan tawayen kasar daukar matakin sasantawa cikin gaggawa.

A watan Maris ne ‘Yan tawayen Mali da mayakan Ansar Dine suka karbe ikon yankin Arewaci bayan sojoji sun hambarar da gwamnatin Farar hula ta Amadou Toumani Toure.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.