Isa ga babban shafi
Rwanda-Congo-Uganda

Rwanda da Uganda suna taimakawa ‘Yan tawayen Congo, inji MDD

Wani Rahoton Majalisar Dinkin Duniya yace gwamnatin Uganda da Rwanda suna taimaka wa ‘Yan tawayen Jamhuriyyar demokradiyyar Congo M23 da ke ci gaba da kashe fararen hula, duk da gwamnatocin kasashen biyu sun musanta zargin.

'Yan tawayen  M23 a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo
'Yan tawayen M23 a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo REUTERS/James Akena
Talla

Majalisar tace ‘Yan Tawayen M23 suna karbar umurni kai tsaye daga Bababn Hafsan tsaron Rwanda, Janar Charles Kayonga, wanda shi kuma ke samun umurni daga Ministan tsaro, Janar James Kabarabe.

Rahoton na asiri da aka tseguntawa kamfanin Dillancin labaran Reuters, yace ita ma kasar Uganda tana goyan bayan ‘Yan Tawayen da ke yaki da dakarun Jamhuriyar Demokradiyar Congo.

Kwamitin masana da kwamitin Sulhu ya kafa don tantance zargin da ake wa Rwanda da Uganda na da hannu wajen tamakawa ‘Yan Tawayen kungiyar M23 a karkashin Janar Bosco Ntaganda, yace babu tantama kasashen na taimaka ma kungiyar.

Bayanan sun ce, yayin da ita Rwanda ce ta taimaka wajen kafa kungiyar, ita kuma Uganda tana bayar da wuri a cikin kasar, don gudanar da aiyukan kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.