Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Boko Haram ta yi tayin sasantawa da Gwamnatin Najeriya

Kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Lidda’awati wal Jihad, da ake kira da sunan Boko Haram, ta fito da wasu bukatu da kungiyar ta ce idan an aiwatar da su za ta kawo karshen kai hare haren da ta ke yi yanzu haka.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan
Talla

A wani sako da kungiyar ta aiko a yanar gizo, mataimakin shugaban kungiyar, Abu Muhammed ibn Abdulaziz, ya ce suna bukatar gwamnati ta cafke tsohon Gwamnan Barno, Ali Modu Sharif, tare da hukunta shi, haka kuma ta bukaci sakin daukacin magoya bayanta da aka kama, tare da gina mu su wasu sabbin Massalatai da matsuguni.

Kungiyar ta bayar da sunayen wasu mutane biyar da ta amince su wakilce ta wajen tattaunawa da Gwamnati, da suka hada da mataimakin shugaban kungiyar, Abu Muhammed Abdul’aziz, da Abu Abbas, da Sheikh Ibrahim Yusuf, da Sheikh Sani Kontagora da Mamman Nur.

Kungiyar kuma ta bukaci gudanar da tattaunawar a kasar Saudi Arabiya, tare da bayar da sunayen wasu dattijai domin shiga tsakani, wadanda suka hada da Tsohon shugaban kasa, Janar Muhammadu Buhari da Dr Shettima Ali Monguno da Senata Bukar Abba Ibrahim da Ambasada Gaji Galtimari da Aisha Alkali Wakil da mijinta.

A sanarwar, Kungiyar ta nisanta kanta daga kashe kashen da ake yi a Maiduguri, inda kungiyar ta danganta al’amarin da siyasa.

A makon nan ne Kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty International, ta zargi jami’an tsaron Najeriya da wuce gona da iri wajen yakin da suka kaddamar don farautar ‘Yan kungiyar Jama’atu Ahlul Sunnah Liadda’awati wal Jihad da ake kira da sunan Boko Haram.

Sai dai kuma a lokacin da ya ke mayar da martani kan rahoton kungiyar ta Amnesty, mai magana da yawun rundunar Sojin Najeriya Kanal Mohammed Yarima ya ce, babu gaskiya a rahoton. Tare da musanta cewar jami'an rundunar Sojin na aikata miyagun ayyuka na cin zarafin Al’umma.

Sai dai kuma Rahoton Amnesty ya zo dai dai da Rahoton Hukumar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch wacce ta yi zargin Jami’an tsaron Najeriya da Kungiyar Boko Haram sun aikata laifukan keta hakkin Bil’adama a rikicin Najeriya da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 3,000.

Rahoton Hukumar HRW da aka fitar mai yawan shafi 98 ya zayyana laifukan keta hakkin bil’adama da Jami’an tsaro da kungiyar Boko Haram suka aiwatar wadanda suka kunshi kisa da gallazawa tare da satar kayayyakin mutane bayan kai hare hare.

An kwashe tsawon lokaci ana fama da hare haren bama bamai a arewacin Najeriya da ake zargin Kungiyar Boko Haram da aikatawa tare da zargin Jami’an tsaro wajen gallazawa tda kisan mutanen da ba su ji ba su gani bad a sunan farautar ‘Yan Boko Haram.

Rahoton Hukumar Human rights Watch ya yi kiran gudanar da bincike tare da neman hukunta Sojoji da ‘Yan Sandan da suka aikata laifin keta hakkin Bil’adama.

Hukumar kuma ta kalubalanci gwamnatin Najeriya game da yin sakaci wajen kula da sha’anin ‘Yan kungiyar Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram dai ta kaddamar da hare hare ne a Najeriya tun bayan kashe shugabanta Muhammed Yusuf da Jami’an tsaro suka yi a zamanin mulkin Marigayi Ummaru Musa ‘Yar’Adua.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.