Isa ga babban shafi
Masar

An zabi sabon Limamin mabiya Kirista a Masar

A kasar Masar an zabi Bishop Tawadros a matsayin fafaroman kasar wanda zai kasance jagoran mabiya addinin Kirista a yankin gabas ta tsakiya. Bishiop Tawadrso ya gaji Paparoma shenouda ne na 111 wanda ya mutu a watan Maris yana da shekaru 88.

Fafaroma mai rikon kwarya Pope Bakhomious rike da takardar da aka zabi Bishop Tawadros  a matsayin sabon Fafaroman Darikar Katolika
Fafaroma mai rikon kwarya Pope Bakhomious rike da takardar da aka zabi Bishop Tawadros a matsayin sabon Fafaroman Darikar Katolika REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Tawadros ya yi takara ne tsakanin shi da wasu manyan malaman addinin Kirista guda biyu Bishop Raphael da kuma Father Raphael Ava Mina wadanda aka tsakulo sunayensu daga majalisar wakilan majami’u sama da 2,000.

Asalin sunan shi shi ne Wagih Sobhy Bakky Suleiman, an haife shi ne a yankin Delta kuma yanzu shi zai jagoranci tsirarun kiristoci mafiya yawa a yankin Gabas ta tsakiya, kuma zai ci gaba da amsa sunan Tawadros na 11.

Sai dai babban kalubalen da ke gaban sabon bishop din, shi ne jagorantar kiristoci a kasar da tafi kowace yawan al’umma tsakanin kasashen Larabawa, da aka hambarar da tsohon shugaba Hosni Mubarak a shekarar bara, tare da zaben Mohamed Morsi na jama’iyyar Islama a wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.