Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Kotun kolin Afrika ta Kudu ta zargi gwamnatin kasar da hana Dalai Lama Visa

Kotun kolin Afrika ta kudu ta zargi gwamnatin kasar da laifin hana wa shugaban al’umar Tibeti Dalai Lama visar shiga kasar da ya nema a shekarar da ta gabata domin kare huldar diplomasiya da ta kasuwanci tsakaninta da kasar China.

Shugaban Al'ummar Tibeti, Dalai Lama
Shugaban Al'ummar Tibeti, Dalai Lama (图片来源:路透社/Yuriko Nakao )
Talla

Wannan shine karo na biyu da Africa ta kudu ke hana Visa ga Dalai Lama domin shiga kasar,duk da cewa ya kai ziyara kasar har sau uku a baya inda har tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ke karban bakuncin shi,.

Dlamini-zuma wacce ta ke shugabancin kungiyar tarrayar Afrika ta musa da cewa an janye bukatar visar a yayin da take jiran umarni daga hukumar,amman ita kotun ta gano siyasa aka nuna akan lamarin

Wannan ziyarar ana ganin zai bata abotaka tsakanin kasashen biyu wanda ake ganin ya jawo har kasar ta Afrika ta kudu ta hana bawa Dalai Lama visar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.