Isa ga babban shafi
Ghana

Mahama ya lashe zaben kasar Ghana

Hukumar Zabe a kasar Ghana, ta bayyana shugaba John Dramani Mahama, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a karshen mako, inda ya samu kusan kashi 51 na kuri’un da aka kada, yayin da Nana Akufo Addo na Jam’iyar NPP ya samu kashi 47.Kafin bada sakamakon zaben, an yi arangama tsakanin ‘Yan sanda da magoya bayan Nana Akuffo Addo.Zababen Shugaban, John Dramani Mahama, ya bukaci shugabanin kasar da su girmama abinda ‘Yan kasar suka zabarwa kansu.Yayin da yake jawabi bayan sanar da sakamakon zaben, shugaban ya bayyana muryar Yan kasar a matsayin muryar Ubangiji.Jim kadan da bayar da sanarwar nasarar zaben, magoya bayan shugaban mai ci, sun hau titunan kasar, suna ta sowa da bukukuwa.Ya ce lalle an gudanar da wannan zabe cikin nasara da kuma kwanciyar hankali, kuma daukacin Jam’iyun da suka shiga zaben, suna da hanyar tattara sakamakon su, kuma shugabanni ba za su yi abin da zai karya doka ba. 

Zababben Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama
Zababben Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama Wikipedia
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.