Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

‘Yan Tawayen Afrika ta tsakiya sun amince su tattauna da Gwamnati

‘Yan Tawayen kasar Afrika ta tsakiya sun amince da matakin hawa teburin sasantawa da Gwamnati tare da alkawalin dakatar da mallake biranen kasar bayan Gwamnatin ta aike da dakaru domin hana su shiga Bangui babban birnin kasar. kakakin ‘Yan Tawayen Eric Massi yace sun amince su aika da wakilansu zuwa Gabon domin tattaunawa da Gwamnatin kasar.

'Yan tawayen Afrika Ta tsakiya a yankin Damara
'Yan tawayen Afrika Ta tsakiya a yankin Damara AFP / Sia Kambou
Talla

Wani Jami’in Diflomasiya ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP cewa a ranar Takwas ga watan Janairu ne za’a fara zaman tattaunawar tsakanin ‘Yan tawaye da Gwamnati tare da Shugaban kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Denis Sassou Nguesso, a matsayin mai shiga tsakani.

‘Yan tawayen sun bayyana shakkunsu akan shugaba Francois Bozize wanda suka zarga ya dakile cim ma nasara a yunkurin sasantawa da aka yi a shekarar 2007.

Tuni dai ‘Yan tawayen suka karbe ikon wasu manyan biranen kasar tare da tunkarar fadar shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.