Isa ga babban shafi
MALI-AU-NATO

Sojan Mali da na kasashen ketare sun kwato garin Konna daga hannun 'yan tawaye.

Sojojin gwamnatin Mali da ke samun goyon bayan sojojin wasu kasashen duniya, sun samu nasarar kwace garin konna da ke tsakiyar kasar daga hannun ‘yan tawaye. Yayin da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin duniya ke cewa yawan mutanen da wannan yaki ya tilasta wa barin gidajensu a yankin ya kai milyan daya a halin yanzu.

Les ONG craignent que les civils soient les premières victimes de la crise au Mali.
Les ONG craignent que les civils soient les premières victimes de la crise au Mali. REUTERS/Joe Penney
Talla

Wata sanarwa da rundunar sojan kasar ta Mali ta fiyar a dazu dazun nan, ta bayyana cewa a yanzu dai ba bu alamun ‘yan tawaye a kusa da garin na Konna mai tazarar kilomita 700 daga birnin Bamako fadar mulkin kasar.
Kakakin rundunar sojan kasar ta Mali da ke garin Sevare wanda ba ya da nisa da garin Konna, Kanar Didier Dakouo, ya ce kwace birnin ya biyo bayan wani mummunan artabu ne da aka yi tsakanin dakarunsa masu samun goyon bayan kasashen ketare da kuma bangaren ‘yan tawayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.