Isa ga babban shafi
Masar

Al’ummar Masar suna bukin cika shekaru biyu da kaddamar da juyin juya hali

Masu adawa da Gwamnatin Morsi sun shirya gudanar da zanga-zanga domin bukin cika shekaru biyu da fara kaddamar da juyin juya halin da ya ba ‘Yan uwa musulmi damar shugabancin kasar bayan kawo karshen mulkin Hosni Mubarak.

Wani Allon Zanen 'Yan adawa mai dauke da zanen rabin fuskar Hosni Mubarak da Soji da kuma Shugaba Mohammed Morsi
Wani Allon Zanen 'Yan adawa mai dauke da zanen rabin fuskar Hosni Mubarak da Soji da kuma Shugaba Mohammed Morsi REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Rahotanni sun ce mutane sun fara hada gangami a Dandalin Tahrir, cibiyar zanga-zanga a birnin Al Kahira. Wasu rahotannin kuma sun ce a jiya Alhamis ‘Yan sanda sun yi arangama da Masu Zanga-zanga wadanda suka nemi ruguza wani shinge da aka dasa don dakile hanyar zuwa dandalin Tahrir.

Ma’aikatar cikin gida tace ‘Yan Sanda Biyar sun samu rauni a lokacin da suke arangama da masu zanga-zanga.

Zanga-zangar dai ta rabu gida biyu inda ‘Yan adawa suka kira gangamin magoya bayansu domin adawa da shugaba Mohammed Morsi. A daya bangaren kuma Magoya bayan Jam’iyyar ‘Yan uwa musulmi ta Brotherhood suka kira gangamin masoya domin bukin samun ‘Yanci daga mulki Hosni Mubarak wanda ya kwashe shekaru sama da Talatin yana shugabanci a Masar.

A shafin shi na Twitter, Madugun adawa Mohamed ElBaradei, ya yi kira ga Al’ummar Masar su fito domin kammala juyin juya halin da suka kaddamar.

Shugaban Mohammed Morsi ya nemi Al'ummar Masar su gudanar da zanga-zangar lumana domin bukin cika shekaru biyu da samun 'yancinsu tare da watsi da kiran 'Yan adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.