Zimbabwe
Tsvangirai na fatan ganin an yi zaben kasar Zimbabwe a watan Yuli
PRIME Ministan Zimbabwe, Morgan Tsvangirai, ya bayyana fatan ganin an gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yuli mai zuwa, bayan kamala zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar a watan gobe.Mai Magana da yawun Jam’iyar ZANU PF ta Robert Mugabe, Rugare Gumbo, yace matsayin Prime Ministan bai saba da na shugaba Robert Mugabe ba.Ana saran shugaba Mugabe mai shekaru 88 ya sake takarar shugabancin kasar.
Wallafawa ranar: