Isa ga babban shafi
Mali

Za a gudanar da taron kasa da kasa don tallafawa Mali

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da cewa a tsakiyar watan Mayu mai zuwa ne za a gudanar da wani babban taron kasa da kasa domin taimakawa kasar Mali mai fama da radadin yakin basasa.

Wasu 'Yan jarida a kasar Mali
Wasu 'Yan jarida a kasar Mali gdb.voanews.com
Talla

Jose Manuel Barosso, shugaban Hukumar Kungiyar ta Tarayyar Turai ne ya tabbatar da hakan jim kadan bayan wata ganawa da ya yi da Firayi Ministan kasar ta Mali Diango Cissoko a yau litinin a birnin Bruxelles, inda ya ce gudanar da taron ya zama wajibi domin sake gina kasar da ke fama da yakin basasa da kuma rikicin siyasa.

A farkon watan janairun da ya gabata ne dai, kasashen duniya da ke halartar wani taro da aka gudanar dangane da makomar kasar ta Mali a birnin Adis Ababa, suka yi alkawalin bai wa kasar tallafin kudade da yawansu ya kai dalar Amurka milyan 455 domin sake gina ta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.