Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban Najeriya ya yi wa wasu da aka samu da laifi afuwa

Rahotanni daga Najeriya sun ce, Majalisar koli da ta kunshi shugaban kasa, mataimakinsa da Gwamnonin jihohi, sun yi wa wasu ‘Yan kasar Afuwa da aka samu da laifi. A cewar kafar yada labaran PREMIUM TIMES, Shugaba Jonathan da ke jagorancin Majalisar ya yi wa marigayi Janar Shehu musa ‘Yar’Adua da Janar Oladipo Diya da Gwamnan Bayelsa, Depriye Alamesiyegha da Shettima Bulama Afuwa.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Reuters/Eduardo Munoz
Talla

Alhaji Bulama tsohon shugaban Bankin Arewa da Mista Alamieyeisegha tsohon gwamnan Bayelsa dukkaninsu sun taba gurfana a gaban hukumar EFCC da ke yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

Masana dai na ganin wannan matakin na shugaban ya nuna gwamnatin Najeriya ba ta damu da yaki da cin hanci ba a kasar.

Amma Shugaba Jonathan yace ba zai yi nadama ba da matakin yi wa mutanen afuwa. Kamar yadda kakakin shugaban Doyin Okupe ya tabbatar a kafar Telebijin ta Channels a Najeriya.

Shehu musa ‘Yar’Adua da Janar Oladipo Diya wadanda Jonathan ya yi wa Afuwa suna cikin wadanda suka yi kokarin kifar da gwamnatin Marigayi Janar Sani Abacha.

Comrate Shehu Sanin a kungiyar Civil Right Watchs a Najeriya yace ya kamata a ware masu laifuka na siyasa da kuma barayin arzikin kasa. Yana mai cewa shugaban ya yi haka ne don ya wanke maigidan shi Alameiyeseigha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.