An kara kashe wani sojan Faransa daya a Mali
Ma’aikatar tsaron kasar Faransa ta tabbatar da mutuwar wani sojanta daya a Mali inda yanzu haka Faransar ke jagorantar fada da ‘yan tawaye a Arewacin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ministan tsaron Faransa Jean-Yves le Drian, ya ce sojan kasar dan kimanin shekaru 24 a duniya mai suna Alexandre Van Dooren, ya hadu da ajalinsa ne a lokacin yake gudanar da aikin share abubuwa masu fashewa da ‘yan tawaye suka binne a kusa da yankin Tessalit da ke gab da iyakar kasar Mali da kuma Aljeriya.
Har ila yau wasu majiyoyi na kusa da ma’aikatar tsaron ta Faransa, sun ce ko baya ga sojan daya da ya hadu da ajalinsa, akwai kuma wasu sojojin biyu da ke cikin mummunan yanayi sakamakon raunukan da suka sama.
A jimilce dai sojojin Faransa biyar ne suka rasa rayukansu daga lokacin da suka shiga kasar ta Mali domin fada da abin da Faransar ta kira shi da suna ta’addanci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu