Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa-Kamaru

Ministan harkokin wajen Faransa ya ziyarci Najeriya

Fransa da kuma Najeriya sun bayyana aniyarsu ta ci gaba da yin aiki kada-da-kafa domin samun nasarar ‘yantar da Fransawan nan bakwai da aka sace a kasar Kamaru sannan kuma ake kyautata zaton cewa ana tsare ne da su a wani wuri da ke tarayyar Najeriya.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius
Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius REUTERS/John Vizcaino
Talla

Ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya Olugbenga Ashiru wanda ke gabatar da taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Faransa Laurent Fabius jiya asabar a birnin Abuja, ya ce yana daga cikin salon siyasarmu na kin biyan diyya ga ‘yan ta’adda, saboda haka za mu yi iya kokarinmu domin ‘yantardar da wadannan mutane ba tare da sun samu ko da kwalzane ba.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius wanda ya ziyarci kasar Kamaru a ranar Juma’a da ta gabata, a jiya asabar ya gana da shugaban Najeirya Goodluck Jonathan, sannan kuma a lokacin da yake gabatar da taron manema labarai, Fabius ya ce ko shakka babu sun tabo batun garkuwar da ake yi da Faransawan a lokacin wannan ganawa da shugaba Jonathan, kuma suna da kyakkyawar fatar ganin cewa an saki wadannan mutane nan bad a jimawa ba.

Yanzu haka dai ko baya ga mutanen 7 da aka sace a kasar Kamaru, akwai wani bafaranshe daya da ake garkuwa da shi bayan an sace shi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.