‘Yan sandan Masar sun cafke Qaddaf al-Dam, dan uwan Gaddafi na Libya
‘Yan sandan kasar Masar sun cafke Ahmed Qaddaf al-Dam, dan uwan marigayi Kanal Gaddafi wanda Libya ke ruwa a jallo saboda ya taka rawa a tsohuwar gwamnatin kasar. ‘Yan sandan Masar sun ce Qaddaf al-Dam, ya mika kansa ne bayan sun kai samame a gidansa da ke Zamalek kusa da Al Kahira.
Wallafawa ranar:
Kamfanin Dillacin labarai na MENA ya ruwaito cewa za’a mika Qaddaf zuwa ga mahukuntan kasar Libya domin gurfana a gaban kotu.
Wani jami’in Diflomasiyar kasar Libya ya shedawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP cewa mahukuntan kasar sun cafke tsohon Jekadan Libya Ali Maria da Mohammed Ibrahim na hannun damar Marigayi Kanal Gaddafi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu