Isa ga babban shafi
Rwanda-ICC-Congo

Gwamnatin Rwanda ta mika Ntaganda zuwa Hague

An fice da Bosco Ntaganda kwamandan ‘Yan tawayen Jamhuhiriyar Congo daga Rwanda zuwa kotun hukunta laifukan yaki a Hague, bayan ya mika kansa ga ofishin jekadancin Amurka a birnin Kigali. Ministan harakokin wajen Rwanda Louise Mushikiwabo ta yada a shafinta na Twitter cewa sun mika Bosco Ntaganda zuwa Hague.

Janar Bosco Ntaganda, Kwamandan 'Yan tawayen Congo
Janar Bosco Ntaganda, Kwamandan 'Yan tawayen Congo REUTERS/Paul Harera
Talla

A wata sanarwa, Kotun hukunta laifukan yaki ta ICC ta tabbatar da cewa Ntaganda yana kan hanyarsa zuwa kasar Netherlands, tana mai cewa nan ba da jimawa ba ne za ta bayyana ranar da zai fara gurfana a gabanta.

A ranar Litinin ne Ntaganda ya mika kansa a ofishin jekadancin Amurka a birnin Kigali na kasar Rwanda bayan kwashe shekaru 15 yana yaki da gwamnatin Jamhuriyyar Congo.

An mika Ntaganda ne zuwa Hague domin fuskantar tuhumar aikata laifukan yaki da suka hada da tursasawa yara kanana shiga aikin soji da kisa da fyade a lokacin yakin Congo tsakanin shekarar 2002 zuwa 2003.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.